Skip to main content

Posts

Showing posts from January, 2019

RICK ROSS YA SAMU KARUWAN BILIYAN

Shahararan mawakin kasar Amurka Rick Ross ya samu karuwa a yayin da budurwar sa ta haifi da namiji. Wannan shine dan sa na biyu da Brianna Camille. Amma abun mamakin shine sunan da ya baiwa dan sa, Billion. Cikakken sunan dan nasa shine Billion Leonard Roberts. Haka Rick Ross ya sanar a shafin sa na Twitter. “Ku taya ni farin cikin zuwan da na Billion Leonard Robert duniya” a cewar Rick Ross. Mahaifin ya nan yana ta shirye-shirye don ganin cewa dan nasa ya samu duk abun da yake bukata na walwala a duniya. Rahotani yayi nuni da cewa Rick Ross ya biya bashin da hukumar IRS ke bin sa na dalla miliyan daya, cikin   bashin dalla miliyan shida wanda suke bin sa. Wannan zabin sunan bai yi wa wasu dadi ko kadan ba, musamman a dandalin Twitter. Wasu sun mayar da martini ganin cewa ya Rick Ross zai bai wa dansa sunan da ke da alaka da kudi? Kowa dai da kiwon da ya karbe shi. Masu salon Magana sun ce abincin wani guban wani.

LL COOL J DA ICE CUBE ZASU SIYE TASHAR TALABIJIN

LL Cool J yana daya daga cikin wadanda suke shirye-shiryen wajan karawa da juna don siyar gidan talabijin 22 sports channel   wanda aka tilasta wa Disney su siyar, kuma Ice cube ya nuna ra’ayin siyar kamfanin. A cewar jaridar TMZ Sports, Disney sun siye tashar ne bayan wani yarjejeniyar da suka kulla da 21 st Century Fox. Disney su ke da hannun jari mafi rinjaye da kamfanin ESPN, kuma siyan kamfanin zai zamo cewa zasu iya mallakan sauran gidajen talabijin 22 da ke karkashin su, wanda zai basu daman mallakar kasuwar dungurungun. Yarjejeniyar zai kai kimanin dalla miliyan 15 zuwa 25. Sa’an da mawakan biyu ke da ita shine akwai wata hamshakin mai kudi wanda take da ra’ayin siyan kamfanin wato Caroline Rafealian. Sauran yan kasuwan da suke son siyar kamfanin sun kunshi Apollo Global Management, Blackstone Group da Sinclair Broadcast Group. Idan LL Cool J da Ice Cube suka samu nasara, wannan zai basu daman mallakar tashoshin FoxSports San Diego, FoxSports Arizona, Fox

MISSY ELLIOT TA KAFA BABBAN TARIHI

Missy Misdemeanor Elliot tana dab da ajiye wani babban tarihi a mazaunin mawakiya mace ta farko wanda za a shigar da sunan ta cikin babban marubutan kasidu wanda aka fi darraja a cikin shekarar 2017, wanda Associated Press suka rubuto. Bayan da irin nasarorin da ta samu a fannin salon hip-hop da pop, wato wakokin zamani, irin su Get ur freak on, da wakar Lady Marmalade wanda ta rera tare da mawaka irin su Christina Aguilera, Pink, Lil Kim da Mya, wanda wakar ta shafa shekaru da dama ana saurarar ta, Mawakiyar da take rike da lambar yabo na Grammy   za ta iya zama mawakiyar salon rap na uku wanda aka taba karama da wannan babbar lambar.  Za ta zauna kujera daya da mawaka biyu wanda su kacal aka bawa wannan lambar wato Jay Z da Jermaine Dupri Mawakan da suka dau tsawon lokaci wajen rubuta wakokin da suka yi fice, akalla shekaru 20, irin su ne suka cancanta a baiwa wannan lamba na girmamawa. Missy Elliot dai ta yi aiki da mawaka da dama irin su Timberland, Aliyah, Ginuwi

RCA SUN TSAYAR DA AIKI TARE DA R KELLY

Mawakin kasar Amurka wanda ake walakabi da Sarkin R&B wato R Kelly ya fada cikin tsaka mai wuya a wannan lokacin a inda ake zargin sa da laifuka wadanda suka shafi fyade ga mata masu karancin shekaru. Wannan ya biyo bayan da aka saki wani labarin fim mai taken Surviving R-Kelly Docu-series . Gajeren fim din da aka saka ya nuna yanda shi mawakin yake tafiye da al’amurorin sa a duniyar waka, amma mawakin bai taba kallon wannan fim din ba, a sannarwar da ya yi wa manema labarai. A cewar jaridar TMZ, R.Kelly yana aiki karkashin RCA Records wanda ke karkashin Sony Music. Kamfanin RCA sun dakatar da sakin sabbin wakokin mawakin sai baba ya gani. Ko da dai R.Kelly yana da wa’adin sakin kundin fefen ayuka har guda biyu a karkashin su, wasu wadandan suka roka a sakaye sunan su sun ce baza su kasha wasu kudadde nan gaba a kan ayukan sa ba sai an gama binkicen da ake yi a kan R Kelly a jihar ta Georgia. Wannan matakin da RCA ta dauka zai hanna R.Kelly cin moriyar samun

BLACK EYED PEAS SUN SAKI SABON WAKA

Bayan da daya daga cikin kungiyar BlackEyed Peas tayi murabus,wato Fergie, mutane da dama na alwashin cewa kungiyar baza ta cigaba da sakin sabbin wakokin da zasu yi tasiri ba.  Amma sauran yayan kungiyar basu bar wannan raunin ya dame su ba a inda suka cigaba da nuna jajircewar su da kara kulla dankon zumunci mai karfi a tsakanin su. Nan take suka tuna da baya a yayin da suka gayyaci daya daga cikin goggagun mawakan hip-hop, wato Nasir Jones wanda aka fi sani da Nas domin fito da wani sabuwar aiki mai taken Back to Hip-hop .  Sabuwar wakar Black-eyed Peas mai taken Back To Hip-hop Tabbas kungiyar ta Black-Eyed Peas basu gaza a cikin wannar aikin ba domin kuwa sun saki sabuwar kundin fefen wakar su mai taken Masters Of The Sun . Sabuwar Kundin fefen Black-Eyed Peas kenan

BOC - ALLAH YA TSARE ALBUM

BOC MADAKI springed up a surprise by dropping this album at the eve of 2019. The 7-track album consist of productions from different producers with each song having a distinctive style.  Download BOC's ALLAH YA TSARE and listen to it right from the scratch. You need to get your playlist updated as soon as possible. TRACK LIST 1. RITES OF PASSAGE 2. IDAN DA RAI 3. KATAKO 4.  MATERIAL GIRL 5.  WA YA SANI 6.  YAYA DAI 7. ALLAH YA TSARE